Over 10 mio. titler Fri fragt ved køb over 499,- Hurtig levering 30 dages retur

Yabanya Allah YA Fish-She KI Fari

- (littafi Akan Tarbiyya)

Bog
  • Format
  • Bog, paperback
  • 94 sider

Beskrivelse

Na yi tunanin rubuta wannan karamin littafin ne domin in bayar da gudumawa ta a bangaren kyautata tarbiyyar 'ya'yanmu da ma ta al'umma baki-daya cikin harshen Hausa. Da kuma amsa kiran Malamanmu bisa nuna muhimmancin rubuce-rubuce domin yada ilimin Addinin Allah (wato Musulunci). Kuma ina rokon Allah da Ya bani dacewa da yardarSa, kuma Ya taimakamin kan wannan aiki na alkhairi, sa'annan Ya sanya wannan aiki ya zamo mai amfani gare ni da al'umma baki-daya. Na sanyawa littafin suna: "Yabanya, Allah Ya Fish-she ki Fari " ne bisa aron kalmar da a kodayaushe Shugaban Majalisar Malamai ta kasa, ta Kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis-Sunnah (wacce marigayi Ash-Sheikh Isma'ila Idris Bn Zakariyya ya kafa), kuma mai cibiyarta a garin Jos, Naijeriya. Wato Ash-Sheikh Muhammad Sani Alhaji Yahya Jingir (Allah Ya tsare shi, Ya kara masa taimako, kuma Ya saka masa da alheri), yake amfani da ita idan yana nufin kira ga yara, a cikin wa'azinsa, wato ya kan ce: "Yabanya, Allah Ya fish-she ki fari " Asalin ma'anar kalmar "Yabanya" a harshen Hausa ita ce "Shuke-shuke sabbin tashi." Kalmar "Shuke-shuke" kuma shi ne jam'in kalmar "Shuka," wato "Tsiro." A takaice dai kalmar "Yabanya" tana nufin lokacin da shuke-shuke (wato amfanin Gona), suka fara girma, kuma suka yi kyau, suna bayar da sha'awa ga duk wanda yayi dubi zuwa gare su. Anan an daganta yara da shuke-shuke ko amfanin Gona kamar yadda Allah Madaukaki Ya danganta matan aure da gonaki ga mazajen aurensu, inda Allah Madaukaki Yake cewa: "Matan ku gonaki ne a gare ku, ..." (Surar Bakara, Aya ta 223) Ash-sheikh Muhammad bn Aliyu bn Muhammad Ash-Shaukaniy yayi bayani a karkashin wannar Ayar kamar haka: "An kamanta abin da ake jefawa a cikin mahaifarsu na daga maniyyi wanda daga gare shi ne tsatso ke samuwa da abin da ake jefawa a cikin kasa na daga iri wanda daga gare shi ne tsiro ke samuwa; domin kowanne daga su biyun hanyar karuwan abinda ake samu daga gare shi ne." Saboda haka, wannan shi ne dalili ko madogara na kwatanta Yara da Yabanya. Ma'anar kalmar "Fari" a harshen hausa, ita ce masifar rashin samuwar ruwan sama a lokacin Damina. Wanda ruwan saman kuma shi ne abin rayuwar shuke-shuke. Kuma wanda yake a dalilin rashinsa zai iya zama sanadiyyar halakar shuke-shuken idan hakan ta dore. Saboda Allah Madaukaki Yayi bayanin cewa da ruwan sama ne shuka ke tsirowa ko rayuwa. Allah Madauakaki Yace: "(Allah) Shi ne Wanda Ya saukar da ruwa daga sama kuna samun abin sha daga gare shi, kuma daga gare shi ne ita ce yake, kuma a cikinsa kuke yin kiwo. Yana tsirar da shuka game da shi, domin ku, da zaituni da dabinai da inabai, kuma daga dukkan 'ya'yan itace. Lalle ne, a cikin wannan, hakika, akwai abin lura ga mutane wadanda suka yi tunani." (Suratu Nahl; aya 10-11) Saboda haka, daga ruwan sama shuka ke samun rayuwa da sauran Bishiyoyi, da ma Dabbobi, kai har ma da Mutane. Kamar yadda Allah Madaukaki Ya ce: "Kuma Mun sanya daga ruwa, dukkan wani abu mai rayuwa"(Sura ...) Rashin ruwan sama (wato fari) ba karamar masifa ba ce, domin zai sabbaba halakar shuke-shuke, kai da ma duk wani abu mai rai. Don haka ne bisa al'adar Hausawa suke nemawa shuke-shuke tsari daga fari. Saboda haka, ma'anar jumlar "Yabanya Allah Ya fish-she ki fari." Ita ce, a zahirin luggar Hausa, nemawa ko yin addu'a bisa rokon Allah da Ya tsare shuke-shuke daga masifar rashin ruwan sama, wacce zata halakar da su, ta hana su rayuwa, ko ta tauye musu rayuwa mai dadi. Wanda hakan kuma zai hana a samu cin moriyarsu kwata-kwata, ko kuma a gagara samun yadda ake bukata game da su. Daga wannan ne, a hikimar-magana, ake yin amfani da jumlar don yin addu'ar nemawa duk wani abin da yayi kyau tsari daga masifar da zata halaka shi. Bisa wannan sigar ne, Malam yake kamanta "Yara" da "Yabanya," kuma yake kamanta "masifar rashin tarbiyya" da "Fari." Sa'annan yake nemawa yaran tsari daga wannar masifa ta rashin tarbiyya da zata abka musu, ta lalata musu rayuwa, ta hana su amfanar kawunansu, da al'ummarsu.

Læs hele beskrivelsen
Detaljer
  • Sidetal94
  • Udgivelsesdato01-08-2014
  • ISBN139781500710781
  • Forlag Createspace
  • FormatPaperback
  • Udgave0
Størrelse og vægt
  • Vægt149 g
  • Dybde0,5 cm
  • coffee cup img
    10 cm
    book img
    15,2 cm
    22,8 cm

    Findes i disse kategorier...

    Se andre, der handler om...

    Machine Name: SAXO082